Majalisar Dattawan Najeriya ta ce a ranar Litinin ta makon gobe ne za ta fara tantance mutanen da shugaban Bola Tinubu ya tura mata domin naɗawa a matsayin ministoci.
Wannan dai ya zo ne bayan da ƴan ƙasar suka ƙagara su ji wadanda za su kasance ‘yan majalisar zartarwar sabon shugaban.

A ranar Alhamis Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanto jerin sunayen mutum 28 waɗanda shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar domin tantance su.
Yanzu-Yanzu: Sojojin Nijar sun Bayyana Sabon Shugaban Kasar
A tattaunawarsa da sashin Hausa na BBC, ɗan Majalisar Dattijan Najeriya, Sulaiman Kawu Sumaila, ya ce “Duk da dai ba a ƙarasa kawo sauran (sunayen) ba, amma za mu fara tantance 28 da aka gabatar a ranar Litinin mai zuwa, kuma tunda dole ne kowace jiha a samu minista, kamar yadda suka nuna shi ma sauran jerin sunayen ba da daɗewa ba za su gabatar mana da su.”
“Sako sunayen ƴan adawa a cikin jerin sunayen ministoci wani abu ne da zai sake samar da fahimtar juna, a yi aiki tare.” Sanata Kawu Sumaila