Daga Hafsat Lawan Sheka
A jiya Alhamis ne shugaban kasa Bola Tinubu, ya aike da jerin sunayen ministoci 28 ga majalisar dattawan Nigeria, domin tantance su a kokarin da yake yi na cika wa’adin kwanaki 60 da kundin tsarin mulkin ƙasar ya kayyade masa.
Jaridar Kadaura24 ta yi nazari kan jerin sunayen wadanda aka aikawa majalisar, da kuma jihohin da suka fito, inda ta gano cewa jihohi 11 ba su da mutum ko daya a cikin sunayen ministocin da aka tura zuwa yanzu .

A cewar sashe na 147(3) na kuskwararren kundin tsarin mulkin Nigeria na 1999, “Shugaban kasa zai nada a kalla Minista daya daga kowace Jiha, wanda zai zama wakilin jiharsa a zauren majalisar zartarwar ta kasa .”
Bisa jerin sunayen da shugaban kasa ya aikewa majalisar, jihohin Katsina, Cross River, da Bauchi suna da ministoci bibiyu, yayin da jihohi 11kuma basu sami ko da mutum daya ba ya zuwa yanzu.
Ministoci: Dalilin da yasa Tinubu bai tura sunan kowa daga Kano ba
Jihohin goma sha daya sune Adamawa, Bayelsa, Gombe, Kano, Kebbi, Kogi, Plateau, Lagos, Osun, Yobe, da Zamfara.
Matan da aka nada a matsayin ministoci wadanda suka yi aure akan dauko su ne daga jihohinsu, in ban da Ngozi Okonjo-Iweala, wadda aka zaba a jihar Abia (jihar mijinta) a shekarar 2003.
Da dumi-dumi: Muhammad Bozoum ya Magantu Bayan yi Masa Juyin Mulki
Ga jerin sunayen ministocin da aka nada da jihohinsu:
Abubakar Momoh – Edo
Yusuf Maitama Tuggar – Bauchi
Ahmad Dangiwa – Katsina
Hanatu Musawa – Katsina
Uche Nnaji – Enugu
Betta Edu Cross – Rivers
Doris Uzoka – Imo
David Umahi – Ebonyi
Nyesom Wike – Rivers
Mohammed Badaru – Jigawa
Nasiru El-Rufai – Kaduna
Emperikpe Ekpo – Akwa Ibom
Nkiru Onyejiocha – Abia
Olubunmi Tunji-Ojo – Ondo
Stella Okotete – Delta
Uju Ohaneye – Anambra
Bello Mohammed Goronyo – Sokoto
Dele Alake – Ekiti
Lateef Fagbemi —Kwara
Mohammed Idris – Niger
Olawale Edun – Ogun
Adebayo Adelabu – Oyo
Imaan Sulaiman-Ibrahim – Nasarawa
Ali Pate – Bauchi
Joseph Utsev – Benue
Abubakar Kyari – Borno
John Enoh – Cross River
Sani Abubakar Danladi – Taraba
Ana sa ran shugaba Tinubu zai aika da karin jerin sunayen ga majalisar dattawa domin cika sharuddan tsarin mulki.