Daga Hafsat Lawan Sheka
Wani lauya mai zaman a jihar Kano wanda dake rajin kare hakkin Dan Adam Barr. Badamasi Suleiman Gandu, ya rubuta takardar korafi ga kwamishinan yan sandan jihar Kano inda ya bukaci rundunar yan sandan jihar ta binciki masu daukar bidiyon wani A. A. Rufa’I wanda yake ikirarin yafi kowa kudi a duniya.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito A. A Rufa’I a kwanakin baya yayi ikirarin siyan Kano da Kaduna da Birnin Dubai da kasar Saudia da kuma wasu mayan kungiyoyin kwallon kafa kamar Real Madrid da Manchester United.
Kotu ta tabbatar da Hanga a matsayin Sanatan Kano ta tsakiya, ta kori karar APC
Majiyar Kadaura24 ta justice watch ta rawaito takarar korafin ta kuma bukaci kare hakkin AA Rufa’I da kuma lafiyar sa sakamakon yada bidiyonsa na kara kawo tasgaro a kokarin da ake na kula da lafiyar sa.

Cikin kunshin takarar korafin wacce Barr. Badamasi Gandu ya sanyawa hanu mai dauke da kwanan watan 24 ga watan Yulin, 2023 wacce kuma aka aikewa Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, lauyan ya roki gwamnatin jihar Kano ta ceto A. A. Rufa’I daga halin da aka sanya shi a ciki.
Takadar Mai taken “Korafi Kan Masu Daukar Bidiyon A. A. RUFA’I” ta ce kamar yadda Allah ya Azurta Kano da Aliko Dangote da Abdussamadu Isyaka Rabi’u, haka ya Azurta ta da A. A. Rufa’I wanda yake ikirarin yafi kowa kudi a duniya sakamakon rashin lafiyar da yake fama da shi.
Lauyan ya bukaci Kwamishinan yan sandan jihar Kano da bada umarnin binciken masu dauka da kuma yada Bidiyon Mista Rufa’I domin kuma doka ta bada damar al’umma su kai rahoton duk wanda yake daukar bidiyon kuma gaza yin hakan sabawa doka ne.
Barista Badamasi Suleiman Gandu dai ya ce ya rubuta takarar korafin ne dogaro da sashi na 12 (1) na dokar kare lafiyar dan Adam na shekarar 2021 da kuma dokar kare lafiyar kowanne Dan kasa a sashi na 12 (2) (b).