Al’adun Bahaushe: Shin ko kun San Al’adar Bahaushe ta zuwa gida rainon ciki da haihuwa ?

Date:

Daga Wasilah Ibrahim Ladan

Ina dalibai da masu neman sanin ilimi game al’adun Bahaushe?

Daga wannan makon ni Wasilah Ibrahim Ladan zan fara gabatar muku da bayanai game da al’adun Malam Bahaushe, Inda a duk mako zamu rika daukar al’adun daya bayan daya domin yi muku bayani akan su.

 

Fatan dai shi ne ku biyo ni sannu a hankali domin sanin wasu al’adun Bashaushe wadanda suka shude dama wadanda har yanzu ana dabbaka su.

 

Ma’anar Al’ada:

Talla

Kalmar Al’ada ta sami ma’anoni daga
masana daban-daban. Alada, abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya. Ta kuma shafi yanayin rayuwar al’umma da harkokin da suke yi don
zaman duniya. Amma a dangane Hausawa kuwa, a wasu wuraren Musulunci da al’adun Larabawa ne suke shiga cikin al’adun Hausawa, wasu wuraren kuma, su al’adun Hausawa ne suke shiga cikin wani abu da Musulunci ya kawo.

 

A wannan makon zamu fara ne da bayana maku yadda ake zuwa gida rainon ciki da haihuwa shekaru masu yawa da suka wuce…

Yunkurin rushe gidaje: Kotu ta ci tarar gwamnatin Kano

Bayan mace ta dauki ciki a bahaushiyar al’ada , ana lura da ita har sai cikin ya kai wata uku ko hudu , sai a hada mata kayayyakin ta da take bukata sai a maida ita gidansu, Inda zata kasance karkashin kulawar kakanninta har sai ta haife abin dake cikinta. Tsowon wannan lokaci za’a bata kulawa ta musamman tare da koya mata wasu muhimman abubuwa wadanda za su taimake ta bayan ta koma gidan mijinta bayan ta yi arba’in.

Kadan daga cikin abubuwan da ake koya mata.

* Yadda zata Kula da lafiyar ta da ta Dan cikinta

* Ire-iren abinci masu gina jiki wadda mai juna biyu ke bukata.

* Ire-iren aikace-aikacen da zata yi da wanda bai kamata ta yi ba

*Irin zaman da ya kamata da ita da yadda zata kwanta.

Amfanin Dauɗar Kunne Da Illar Ƙwaƙwale ta -Daga Masana

Bayan tafiya ta yi nisa akwai wasu ‘yan jike-jike na magungunan gargajiya a al’adar Bahaushe da ake tanadarwa mai dauke da juna biyu wanda zata rika sha lokaci lokaci har sai ta haihu,

Duk a wannan lokacin za a koya mata yadda zata gudanar da zamantakewarta da mijinta domin lokacin da aka aurar da ita tana da sauran yarinta kuma tana karkashin kulawar wadda aka hadata da ita .

Haka nan kuma zata koyi yadda zata yi rainon ciki da abun da zata haifa.

Abun mamaki anan shi ne duk tsawon wannan lokaci, mijin ta zai dinga zuwa tare da kawo mata asafi amma ba za’a barsa ya gana da ita ba sai dai iyayensa ko yan’uwansa, sune kadai zasu ganta, ana haka ne har nakuda ta zo , a haife lafiya sai a shiga tsarabe-tsaraben haihuwa, bayan ta sauka lafiya za a sanar da mijin Inda za a yi masa albishir.

Kadan daga cikin shirye-shiryen abubuwan da angon qarni zai yi sun hada da

*Naman kauri

*Kayan barka

*Ragon suna(hakika)

*Abinci da za’a ci ranar suna

Haka dai za’a cigaba da lura da ita har sai ta yi arba’in wato kwanaki 40, to daga nan ne za’a bata damar zuwa gidajen yan uwa da abokan arziki, kuma ita wannan ziyarar a al’adar Bahaushe sunan ta yawon arba’in. Daga bisa ni Kuma a mayar da ita gidan mijinta bayan iyayen ta sun yi mata hidima iri-iri .

Alhamdulillah, Mu hadu wani makon

Daga Wasilah Ibrahim Ladan

Masaniyar tarihi da al’adun Hausawa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...