Daga Rahama Umar Kwaru
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bukaci gwamnatocin jihohi da na tarayya da su samar da cibiyoyin koyar da sana’o’i a jami’o’i domin magance matsalar karuwar rashin aikin yi da ya addabi kasar Nigeria.
“A kowace shekara jami’o’i da manyan makarantu na yayi miliyoyin wadanda suka kammala karatu ba tare da aikin yi ba, kuma halin rashin aikin yi a Najeriya ya sanya akasarin daliban da suka kammala karatu cikin Takaici”. Inji Shekarau

Sanata Shekarau, ya yi wannan kiran ne a wajen rufe bikin horas da matasan jahar Yobe sana’oi da gidauniyar Sir Ahmadu Bello, da hadin gwiwar gwamnatin jihar Yobe ta kuma tallafa musu da kudade domin bunkasa sana’o’insu.
“A cikin shekaru da yawa da suka gabata, ƙalubalen kasar nan shi ne rashin aikin yi ga matasa, kuma mafita ita ce koma wa kan sana’oi. A yau muna da wadanda suka kammala karatun digiri da digiri na biyu, da Ph.D. Masu yawa wajen neman aikin yi”. A cewar Shekarau
Al’adun Bahaushe: Shin ko kun San Al’adar Bahaushe ta zuwa gida rainon ciki da haihuwa ?
“Sakona ga gwamnatin tarayya shi ne a samar da cibiyoyi a jami’o’i, manyan makarantu Wanda za su bullo da wani bangare na horar da Dalibai sana’oi domin a lokacin da suka kammala karatu a fannoni daban-daban suna da wasu sana’o’in da za su je don fara rayuwa a kansu,”
Tsohon Ministan Ilimi wanda shi ne Sakataren Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello yayi kira ta ga Gwamnatin Yobe, da ma gwamnatocin Jihohin Arewa dasu jajirce wajen kawar da talauci da kuma magance wasu matsalolin da suka addabi yankunan mu.
Abin da gidauniyar ke yi a yanzu shi ne Taimakawa Matasa da suke da kwarewa a wani fanni na Sana’a don su samu Dogaro da kai ,tare da kara wayar musu da kai.Don haka na tabbata duk wadanda aka horar za su je su horar da wasu kuma za su kara daukar ma’aikata,” inji Sanata Shekarau
Amfanin Dauɗar Kunne” Da Illar Ƙwaƙwale ta – Daga Masana
A nasa jawabin, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya ce dole a dawo kan tsari irin nasu Sardauna, a yanzu yankin arewa ya fada cikini talauci sakamakon rashin shugabanci, ga rashawa da rashin shugabanci na gari.
Buni wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Hon Idi Barde Gubana, ya ce domin al’amura su daidaita a yankin ya bukaci yaki da talauci tare da saka jari a fannin ilimi.
Yayin da sauran yankunan kasar ke gudun talauci, jihohin arewa kuma sun rungumi talauci. Muna bukatar abin da zai hada kan Arewa ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa ko kabila ba.