Daga Kamal Umar Kurna
Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Amb. Alhaji Ahmadu Haruna Zago, yace hukumar sa zata yi amfani da sashin dokar ma’aikatar wajen tursasawa tare da magance dabi’ar zubar da shara da tsakar dare a wuraren da basu kamata ba a jihar nan.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai sanda ma’aikatan hukumar suke tsaka da aikin kwashe sharar dake fagge ‘yan Alluna.

Ambasada Dan zago yace abin takaici ne yadda wasu suke bin tsakar dare suna jibge sharar akan titunan jihar nan da wuraren da basu dace ba musamman wuraren da aka kwashe sharar tun da farko.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya nada shugabannin wasu Ma’aikatun Lafiya a Kano
A bayanansu tunda farko mazauna kasuwar ta ‘yan fagge ‘yan Alluna sun yaba da yadda aikin kwashe sharar yake gudana a fadin jihar nan Koda dai wasu daga cikin su sun bayyana cewa kamata gwamnati ta gudanar da aikin tuntuni.
Daga cikin wuraren da hukumar kwashe sharar tayi aiki a yau sun hada da fagge ‘yan Alluna, karkashin gadar kasuwar Bata da New Road dake Unguwar Sabon Gari.