Daga Hafsat Lawan Sheka
Kungiyar ‘yan jaridun Kano masu kafafen yada labarai a yanar gizo ta yi kira ga mambobinta da su kiyaye ka’idar aikin jarida da ke jagorantar wannan sana’a a kowanne lokaci.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Yakubu Salisu ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24 bayan wani taro da kungiyar ta gudana a ranar Asabar a Kano.

A cewarsa, a matsayinsu na kwararru, ya kamata a ko da yaushe su yi kokarin wajen baiwaa al’umma ingantattun bayanai na gaskiya da adalci da kuma maslahar jama’a.
Ya ce, a daidai lokacin da dandalin sada zumunta ya zama wajen yada labaran karya, ya kamata ‘yan jaridun dake da kafafen yada a dandalin su Maida hankali wajen yada labarai na gaskiya da ilimantar da jama’a don inganta rayuwar su.
Yanzu-Yanzu: Yadda Tinubu zai samar da hukumar kula da farashin abinci a Nigeria
Yakubu Salisu ya baiwa al’umma tabbacin cigaba da samun sahihan labarai daga jaridun ‘ya’yan kungiyar wadanda suke aikinsu bisa kwarewa da ka’idojin aikin jarida.
Ya kuma kara da cewa a matsayinsu na kwararru, kungiyar za ta ci gaba da horar da ‘ya’yanta da kuma horar da su kan sabbin dabarun da za su kara taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.
Ya yi kira ga gwamnati da daidaikun jama’a, kungiyoyi da kamfanoni da su taimaka wajen yaki da ta’addanci a fagen yada labarai, musamman ta hanyar tantance ‘yan jaridu na gaskiya ba wai kawai duk wanda ya yanke shawarar gudanar da harkar yada labarai a yanar gizo ba, wadanda suke aikin su ba tare da wani satifiket a fagen aikin jarida ba.