Zargin Almundahana: Kotu ta bayar da umarnin sakin tsohon kwamishinan Ganduje

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Babbar kotun tarayyar da ke Kano ta ba da umarnin a saki wani tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Idris Wada Saleh wanda ake zargi da almundahanar naira biliyan ɗaya.

 

An zargi tsohon kwamishinan da yaudara da kuma yin karya a takardun wasu ayyuka zamanin gwamnatin da ta wuce ta Abdullahi Umar Ganduje.

Talla

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a baya-bayan nan ne babbar kotun Majistaren jihar ta umarci tsare shi a hannun hukumar karɓar ƙorafe- ƙorafe hana cin hanci ta jihar Kano (KPCACC).

Wani Fursuna da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai ya kammala Digirinsa na 2 a Gidan Yari

Hukumar karɓar korafe-korafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta yi zargin cewa a 2023, tsohon kwamishinan ya bai wa kamfanin Arafat construction da ‘Multi resources’ kudi nairan biliyan ɗaya domin gyaran tituna 30 a cikin birnin jihar.

To sai dai in ji hukumar, babu ko ɗaya cikin ayyukan da aka yi. A baya-bayan nan dai hukumar KPCACC ta ce ta aike da takardar gayyata ga tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje a kan ‘bidiyon dala’.

To amma babbar kotun tarayya a jihar ta dakatar da hukumar a kan wannan batu, har zuwa lokacin da za ta kammala sauraron ƙorafin da Ganduje ya shigar gabanta yana neman ta hana hukumar binciken sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...