Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’ummar jihar kano dama kasa baki daya da su himmatu wajen dasa itatuwa don kaucewa kwararowar hamada.
” A irin wannan yanayi da ake fuskantar chanjin yanayi yana da kyau al’ummar mu su kaucewa sare bishiyoyi, a maimakon hakan ku mai da hankali wajen dashen itatuwa a muhallanku da sauran wuraren don bai gwamnati damar magance kwararowar hamada da dumamar yanayi”.

Mai Martaba Sarkin ya bukaci hakan ne lokacin da ya karbi ayarin shugabanin gudanarwa na Hukumar Kula da dazuzzuka da kwararowar hamada ta kasa karkashin jagorancin mataimakin shugaban hukumar Alhaji Auwalu Inusa Yusuf da suka kai masa ziyara a fadarsa.
Da dumi-dumi: Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Hafsoshin tsaron Nigeria
Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa ya zama wajibi ga al’ummar kasar nan musamman manoma dasu kaucewa sare itatuwa barkatai ba bisa ka’idaba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24.
Shi ma a nasa jawabin mataimakin shugaban hukumar Alhaji Auwalu Inusa Yusuf, yace sun kaiwa Sarkin ziyarar ne domin gaisuwar bangirma tare da neman tabarakin Sarki duba da cewa wannan ranace ta bikin dashen itatuwa ta duniya wadda ake gudanar da ita a duk shekara kuma a fadin duniya.