Ilimi Dole: cheche-ku ce ta kaure tsakanin tsoho da sabon kwamishinan Ilimi a Kano

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
 Gwamnatin da ta shude a jihar Kano ta ce ya kamata gwamnati mai ci ta jam’iyyar NNPP ta yi nazari a kan takardar manufofinta na ilimi kyauta kuma dole kafin ta yi suka a kanta.
 Tsohon kwamishinan ma’aikatar ilimi, Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru ya bayyana haka yayin da yake mayar da martani ga sabon kwamishinan ilimi Hon. Umar Haruna Doguwa, ta cikin wata sanarwa da ya aikowa kadaura24.
Talla
Kadaura24 ta rawaito Doguwa dai ya ce  tsarin ilimi kyauta daga firamare zuwa sakandare da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bari a baya na da tarin kura-kurai.
“Ya kamata ka zauna ka nazarci daftarin manufofin Ilimi kyauta domin masana a fannin ilimi da kungiyoyin masu zaman kansu da da sauran yan takarda ne suka zauna suka tsara shi, idan ka fahimci su idan ya so sai ka yi suka”. Kiru ya shawarci Doguwa
  Kiru ya kuma yi kira gare shi da ya zage damtse wajen samar da muhimman abubuwan da ake bukata a makarantun da ke karkashin ma’aikatar maimakon mayar da hankalinsa wajen sukai abun da bai fahimta ba.
 “Na yi Allah-wadai da kakkausar murya, bisa kalaman da abokina kuma dan uwana ya yi dangane da manufofin ilimi da muka bari a baya, Ina ganin watanni biyu sun yi kadan ga akilar gwamnati ta fara sukar manufofin da masana harkokin Ilimi suka tsara,” a cewar Kiru
 Tsohon kwamishinan ya ci gaba da cewa, abin takaici ne matuka yadda sabon kwamishinan yake amfani da dalilai na siyasa wajen yin Allah wadai da wani tsari da shi kadai ba zai iya samar da shi ba.
 Ya kara da cewa wannan yunƙuri da gwamnatin NNPP ta yi na sanya fannin ilimi cikin halin kaka-ni-kayi na siyasa, manufa ce da gangan don lalata nasarorin da Ganduje ya samu a tsakanin 2015 zuwa 2023 na gwamnatinsa.
 Kiru ya bayyana cewa ya kamata gwamnatin NNPP ta dakatar da sanya Siyasa cikin harkokin Ilimi da nufin kawo cikas ga nasarorin da gwamnatin Ganduje ta samu a cikin shekaru takwas da suka gabata.
 Tsohon kwamishinan ya bayyana cewa a shekarar 2015 lokacin da gwamnatin APC ta hau karagar mulki, ta tarar da tsarin ilimi wanda bai dace da tsarin cigaba makarantu da samar da ababen more rayuwa a makarantu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...