Wani Fursuna da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai ya kammala Digirinsa na 2 a Gidan Yari

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Wani fursuna da aka yankewa hukuncin daurin Rai da Rai a gidan yari a Awka dake jihar Anambra, Jude Onwuzulike, ya samu kammala digirinsa na biyu a Jami’ar Jami’ar Karatu daga gida ta Najeriya (NOUN).

 

An ba shi satifiket a ranar Juma’a bayan an tabbatar da ya cewa ya koyi abun da aka koya masa da kuma da’a .

Talla

Fursunan ya kammala karatunsa na digirin farko a fannin Ilimi.

Ilimi Dole: cheche-ku ce ta kaure tsakanin tsoho da sabon kwamishinan Ilimi a Kano

Da yake jawabi, Onwuzulike, wanda ke cike da farin ciki, ya gode wa jami’ar NOUN wadda ta basu damar yin karatu duk da suna daure .

Daily trust ta rawaito fursunan ya kuma yabawa uwargidan sa (Matarsa) akan duk irin goyon bayan da take bayarwa.

“Lokacin da na zo nan, ban san akwai irin wannan damar ba. Ina tsammanin a ƙasashen da suka ci gaba ne kawai ake samun irin wannan damar. Na shigo nan da satifiket kawai, amma yanzu ina da guda uku, kuma a shirye nake in samu wani kafin in tafi.

“Ga ’yan uwana fursunoni, ina so ku dauki wannan daurin da akai muku a matsayin wani tsani. Ku yi Lokaci yi rajista, za ku iya ci gaba da karatun ku ko da an sallame ku, tabbas idan kuka yi haka ba za ku taɓa yin nadama ba, ”in ji shi.

Da take jawabi yayin gabatar da takardar shedar kammala karatun, Darakta NOUN, Cibiyar Nazarin Awka, Dokta Scholastica Ezeribe, ta bayyana jin dadinta yadda fursunonin ke sha’awar ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku ba da gudunmawa kano ta zauna Lafiya – Waiya ya shawarci yan jaridun yanar gizo

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci kafafen yada labarai na...

KAROTA ta tabbatar da aniyarta na inganta matsayin jami’anta

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano...

Sarkin Sanusi ya amince da nadin sabon mai unguwar Hotoro GRA

  Mai martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi...