Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu ƙaruwar talauci a matalautan kasashe, inda adadin mutanen da ke rayuwa ƙasa da dala 3.65 a shekarar 2023 ya kai miliyan 165.
Rahoton ya ambato shugaban Hukumar UNDP Achim Steiner ya ce ”Kasashen da suka zuba jari cikin shekaru uku da suka gabata, domin tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi, sun taimaka wajen kare al’ummarsu da dama daga faɗawa ƙangin na talauci.

BBC Hausa ta rawaito Cikin wani rahoton da Hukumar Raya Ƙasashe Ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP ta fitar ranar Alhamis, ya ce annobar Korona da hauhawar farashi da kuma yaƘin Ukraine sun tilasta wa mutum miliyan 165 shiga Ƙangin talauci tun shekarar 2020 zuwa 2023.
Yanzu-Yanzu: Yadda Tinubu zai samar da hukumar kula da farashin abinci a Nigeria
A yayin da ya ce ƙasashen da ba su yi wani hoɓɓasa wajen rage talaucin suka fi fuskantar matalar ƙaruwar matalauta a cikin al’ummominsu.
Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma yi kiran a sassauta wa ƙasashe masu tasowa biyan bashi.
”A yau ƙasashe 46 na kashe fiye da kashi 10 na kuɗin shigar da suke samu wajen tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a ƙasashen”, in ji shi.
A cewar rahoton biyan bashi da ƙasashen ke yi na ƙara musu wahalhalu wajen tallafa wa talakawan cikinsu a bangarorin lafiya da ilimi da sauran bukatun rayuwa.