NCAA ta dakatar da wasu jiragen Max Air daga aiki a Nigeria

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Hukumar kula da sufurin jirgin sama ta Najeriya NCAA ta ce ta dakatar da ayyukan jirgin sama na Max Air mai ƙirar Boeing 737 nan take.

 

Hukumar ta NCAA ta lissafa abubuwan da suka faru waɗanda har suka sanya ta ɗaukar wannan mataki.

Talla

Da take bayyana dakatarwar a cikin wata sanarwa, Daraktan kula da Ayyuka da Horaswa da kuma ba da Lasisi, Kyaftin Ibrahim Dambazau da kuma Babban Daraktan Hukumar Kyaftin Musa Nuhu suka fitar, hukumar ta ce ta dauki matakin ne saboda wasu al’amura da suka faru da jiragen Max Air ƙirar B737.

Da dumi-dumi: Kotu ta baiwa DSS umarnin ko ta saki Emefiele ko ta gurfanar da shi

A ciki har da lalacewar wilin tayar saukar jirgi ta gaba, da ta janyo wani mummunan al’amari ga jirgin Boeing 737-400 tsakanin tashinsa daga filin jirgin sama a jihar Adamawa zuwa saukarsa a filin jirgin Nnamdi Azikiwe a Abuja ranar 7 ga Mayu, 2023.

Hukumar NCAA ta sake soke tashin jirgin Max ƙirar Boeing 737-400 mai lamba 5N-MBD a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA) saboda fitar iskar gas mai tsananin zafin a jirgin ranar 11 ga Yuli, 2023.

NCAA ta kuma cewa ta kafa wata ayarin jami’an bincike da za su bi diddigi game da harkokin kamfanin na Max Air.

Hukumar ta ce dole sai sun gamsu da sakamakon binciken, kafin ta bai jirgin Boeing 737-400 damar ci gaba da ayyukansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...