Gwamnatin Kano ta bada tallafin Karatu ga masu bukata ta musamman a jihar

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da tallafin karatu zuwa kasashen ketare ga masu bukata ta musamman a jihar.

 

‘’Masu nakasasa, a jihar Kano, wadanda suka cancanta, za su ci gajiyar shirin bayar da tallafin karatu da gwamnatin jihar ta yi kwanan nan zuwa kasashen ketare” a cewar kwamishinan ilimi na jihar, Alh. Umar Haruna Doguwa ya sanar.

Talla

“Yana cikin wani tsari da gwamnatin yanzu ta yi don tabbatar da adalci da samun daidaiton samun ilimi ga kowane dan asalin jihar, daidai da yarjejeniyar kasa da kasa”.

Yanzu-Yanzu: Tinubu ya nemi Majalisar Wakilai ta sahale ya kashe Naira Biliyan 500 don Tallafawa Yan Nigeria

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Ameen K. Yassar ya aikowa kadaura24.

“Tabbas za mu ba da tallafin karatu ga waɗanda ke da digiri na farko da na biyu, kuma zamu hada da masu bukata ta musamman, don ƙarfafa musu gwiwa tare da basu damar amfana da tsare-tsaren gwamnatin kano daidai da kowa”.

Umar Doguwa ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da yake mayar da martani ga wasu jami’an kungiyar Mercy Corps da Coalition of Disabled Self Advocacy Network Group, wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suka ziyarce shi a ofishinsa.

Ya ce “gwamnati za ta kuma duba yiwuwar kafa makarantun masu bukata ta musamman a jihar, duk da cewa za a yi la’akari da cewa ana basu dama tare da kulawa ta musamman a makarantun gwamnati, kuma za’a yi hakan ne domin tabbatar da cewa gwamnatin ta rungumi kowa ba tare da nuna banbanci ba.

Ya jaddada cewa a wani bangare na kudirin tallafawa nakasassu, a kwanakin baya ne gwamnatin jihar ta ba su fom din rajistar NECO guda 150, inda ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da wannan dama ta yadda za su sami ingantacciyar rayuwa.

Tun da farko, Nafisa Amadu Abubakar, Ko’odinetan tsare-tsare da bayar da shawarwari, Mercy Corps da wasu wakilan nakasassu, sun bukaci gwamnatin jihar da ta tallafa wa kungiyar don gudanar da shirin inganta rayuwar su a jihar, tare da tabbatar da cewa masu bukata ta musamman sun shiga duk wasu tsare-tsaren na ci gaba da gwamnatin zata fito da su.

A wani labarin kuma kwamishinan ilimi Alh. Umar Haruna Doguwa, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta hada kai da abokan huldar ci gaba, domin magance matsalolin da ilimi ke fuskanta a jihar, musamman a fannin bunkasa harkar koyo da koyarwa, ilimin ‘ya’ya mata, da samar da ilmi marasa galihu .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...