Babbar kotun jiha da ke Miller Road a nan Kano ta dakatar da gwamnantin Kano daga yin rusau a gine-ginen da ke jikin Badala akan titin zuwa jami’ar Bayero.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Gwamna Engr Abba Kabir Yusuf ta sanyawa masu gine-gine a jikin badala alamar jan fenti wanda hakan ke alamta cewa kowanne lokaci za’a iya rushe gine-ginen, saboda abun da gwamnatin ta kirawo da cewa an yi gine-ginen ne ba bisa ƙa’ida ba.

Wannan na zuwa ne bayan da mamallaka wuraren suka roki kotun da ta duba halin da suke ciki, la’akari da cewar bu sa karya ka’ida ba wajen mallakar wuraren.
Cire Tallafin Mai: Za a yi ƙarin kuɗin burodi a Najeriya
Mai shari’a Hafsat Yahya Sani ce ta bayar da umarnin dakatarwar har sai kotu ta kammala nazari akan al’amarin.
Haka kuma ta sanya ranar alhamis 26 ga Oktoba mai zuwa a matsayin ranar da za a saurari shari’ar.