Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban kasar Nigeria, Bola Ahmed Tinubu ya rubutawa majalisar wakilai wasika, yana neman a yi masa gyara a kwarya-kwaryar kasafin kudin shekarar 2022 domin daukar Naira biliyan 500 domin samar da tallafi ga al’ummar Nigeria.
A ranar Laraba, kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya karanta wasikar shugaban a zauren majalisar.

Abbas ya ce bukatar ta zama dole domin baiwa gwamnati damar samar da tallafi ga ‘yan Najeriya domin dakile radadin cire tallafin man fetur.
Shari’ar zaɓen gwamnan Kano: INEC ta gabatar da na’urar BVAS 21 ga kotu
“Na rubuta wannan wasika ne domin neman a gyara dokar karin kasafin kudin na shekarar 2022. Bukatar ta zama dole a wannan lokaci don samar da kudaden da za’a samar da abubuwan da suka dace don rage radadin cire tallafin man fetur ga ‘yan Najeriya.
“Don haka, an ciro Naira biliyan 500 kawai daga cikin karin kasafin kudi na shekarar 2022 na Naira biliyan 819, 536, 937, 937, 803 kawai don samar da kayan agaji ga ‘yan Najeriya don magance wahalhalun da yan Nigeria suke fuskanta sakamakon cire tallafin,” in ji wasikar.
Ya bukaci yan majalisar da su gaggauta Amincewa da bukatar don baiwa gwamnatinsa damar samar da abubuwan jin kai ga ‘yan Najeriya.
Bayan karanta wannan bukata, kakakin majalisar ya ce majalisar za ta fara nazarin bukatar shugaban a ranar Alhamis.