Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gabatar da na’urorin tantance masu kada kuri’a, wato BVAS, ga Kotun Sauraren Ƙarar Zaɓen Gwamnan Jihar Kano.
An yi amfani da na’urar BVAS ɗin ne a rumfunan zabe 21 da ke kananan hukumomi 10, da su ka haɗa da Tudun-Wada, Gaya, Gezawa, Bunkure, Bebeji, Ungogo, Ajingi, Warawa, Karaye da Garko.
NEMA ta buƙaci gwamnoni su zauna cikin shiri kan yiwuwar samun ambaliya
A ranar 9 ga watan Afrilu jam’iyyar APC ta shigar da korafi, ta na kalubalantar INEC kan ayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.
Wadanda APC ta ke ƙara sun haɗa da INEC, Abba Kabir Yusuf da kuma jam’iyyar NNPP.

Kotun, a ranar 6 ga watan Yuni ta bai wa mai shigar da kara izinin shiga tare da duba na’urorin BVAS da INEC ta yi amfani da su a zaben gwamna.
A ci gaba da zaman sauraron shari’ar, Lauyan Hukumar INEC, E.A. Oshayomi ya jagoranci Ocheka, ma’aikacin INEC, ya gabatar da na’urorin ga kotu.
Ocheka ya shaida wa kotun cewa na’urorin BVAS na bukatar kariya domin idan batirinsu ya lalace sai an aika zuwa China kafin a sake samun wasu.
Don haka ne ya nemi da ya koma da na’urorin na BVAS saboda uzuri na kariya.
Lauyan mai kara, Nureini Jimoh, SAN, ya mika BVAS 21 ga kotun a matsayin hujja ga ƙorafin da su ka shigar, ya kuma nuna rashin goyon baya ga mayar da na’urorin ga INEC.
Tsaftar Muhalli: Zamu haɗa kai da shugabannin kasuwani a kano – Amadu Danzago
Lauyan Abba Kabir Yusuf, R A Lawal, da kuma Lauyan NNPP, John Baylesha, ba su yi adawa da amincewar na’urorin BVAS a cikin shaida ba.
“Da zarar mai shigar da kara ya ba da na’urorin, yanzu ya rage ga kotu ta yanke shawarar inda za ta ajiye su saboda dalilai na kariya,” in ji shi.
NAN ta ruwaito cewa kawo yanzu mai shigar da kara ya gabatar da shaidu 18 da za su ba da shaida a gaban kotu domin tabbatar da karar ta.
Kwamitin sauraron karar na mutum uku, karkashin jagorancin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ya ɗage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 12 ga watan Yuli.