Daga Rahama Umar Kwaru
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya bayyana dalilin da ya sa aka dauki lokaci mai tsawo kafin shugaba Bola Tinubu ya bayyana sunayen sabbin ministocinsa.
Da yake magana a ranar Litinin a Abuja, yayin ganawarsa da shugabannin jam’iyyar APC a fadin kasar Nigeria, Adamu ya bayyana cewa Tinubu ya na tuntuba sosai kafin ya yanke shawarar sunayen wadanda zai zaba.

“Shugaban kasa yana tuntubar wadanda suka dace sosai kafin ya fito da wadanda zai nada a matsayin ministoci.
“Za a fara fito da sunayen wadanda za’a nada a mukaman ministocin, sannan za’a tantance su kuma a sake mayarwa Shugaban kasa sunayen daga bisani kuma a bayyana sunayen .
“Kuma mai girma shugaban kasa zai nada ministocinsa a hukumance ya rantsar da su.
“Bayan ya yi hakan ne zai bayyana sunayensu tare da bayyana ma’aikatun da za’a tura su, hakan kuma a lokacin za’a gane zai rage ma’aikatu ko zai bar su a yadda suke.” in ji Adamau