Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Tsohon shugaban kasar Nigeria Muhammadu Buhari ya karyata labarin da ke cewa ya bar kasar domin gudun hijira .
Buhari ya ce labarin ba shi da tushe ballantana makama .
Da yake magana a madadin tsohon shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce Buhari ya karyata labarin domin ya dawo gida Daura dake jihar katsina tare da iyalan sa .

” Ya kamata a ce kowacce jarida ta tantance labarin kafin ta buga shi, kamar yadda yake a ƙa’ida”.
Kwanan nan Buhari ya je London, kuma yayin ziyarar ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu.