Daga Hafsat Lawan Sheka
Hukumar kula da tituna ta ƙasa wato FERMA, ta ce ta fara shirin cike ramuka tare da gyaran hanyoyin da suka lalace a fadin kasar nan yayin da damina ta shigo.
“Ya zama wajibi a dauki matakin ne saboda bukatar da ake da ita na rage wahalhalu da tsaikon da direbobi ke fuskanta a tituna a kullum a fadin Nigeria.

Manajan-Darakta na riƙo na hukumar ta FERMA, Godson Amos ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a yau Lahadi a Abuja.
Ya bayyana kwarin gwiwa cewa za a samu nasarar aikin a cikin makwanni shida, kuma za a yi aiki cike da dukkanin ramuka da gyara lalacewar hanyoyi, kan manyan tituna a fadin kasar.
Ya ce ya samu rahotanni a fadin kasar nan na lalacewar manyan tituna da ke fadin kasar, wanda a cewar sa, ya jawo wa masu amfani da hanyoyin matsala.
Ya kara da cewa lalacewar na kawo cikas ga harkokin tattalin arziki saboda yadda jama’a ba su iya kwashe kayayyaki daga wannan wuri zuwa wancan.