Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Shugaban majalisar wakilan Nigeria Tajudeen Abbas, a ranar Talata ya bayyana sunayen sabbin shugabannin majalisar wakilai ta 10.
Zargin Almundahana: Hukumar yaƙi da cin haci ta kama kwamishinan Ganduje da wasu mutane 5
Wadanda Shugaban majalisar ya sanar Sun hada da Julius Ihonvbere (APC – Edo, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai), Halims Abdullahi (APC – Kogi, mataimakiyar shugaban masu rinjaye), Bello Kumo (APC – Gombe, mai tsawatarwa Chief Whip), Adewunmi Onanuga (APC – Ogun, mataimakin Mai tsawatarwa ).

Abbas ya kuma karanto wata wasika daga ɓangaren marasa rinjaye na majalisar, Inda suma suka bayyana sunayen wadanda zasu Jagorance su a majalisar.
Yanzu-Yanzu: Godswill Akpabio ya bayyana sunayen sauran Shugabannin Majalisar Dattawan Nigeria
Wasikar ta bayyana Kingsley Chinda (PDP, shugaban marasa rinjaye), Aliyu Madaki (NNPP, mataimakin shugaban marasa rinjaye), Ali Isah (PDP, mai tsawatarwa marasa rinjaye), da George Ebizimawo (Labour Party, mataimakin mai tsawatarwa marasa rinjaye).