Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Wasu Yan majalisar tarayya na jam’iyyar NNPP daga jihar kano, Sanata Rufi’i Sani Hanga Dan majalisar dattawa mai wakiltar kano ta tsakiy da Aliyu Sani Madakin gini, Dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Dala sun rabauta da nukamai a majalisa ta goma .
Kadaura24 ta rawaito a safiyar wannan rana Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya bayyana sunayen sauran Shugabannin Majalisar Dattawan, Inda a cikinsu ya bayyana Sanata Rufi’i Sani Hanga a matsayin mataimakin mai tsawatarwa marasa rinjaye na majalisar.

Hakan shi ma Shugaban majalisar wakilai Tajuddeen Abbas ya ambata sunan Dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Dala Aliyu Sani Madakin gini a matsayin mataimakin Shugaban marasa rinjaye na majalisar.
Dama dai dukkanin an tsammaci wadannan yan majalisu zasu iya rabauta da mukamai a majalisa ta goma, saboda irin rawar da suka taka wajen zabar sabbin shugabannin majalisun biyu.
Yanzu-Yanzu: Godswill Akpabio ya bayyana sunayen sauran Shugabannin Majalisar Dattawan Nigeria
Anfi kyautatawa Aliyu Sani Madakin gini zaton samun mukami saboda yadda ya bada gudunmawa sosai wajen ganin Tajuddeen Abbas ya zama Shugaban majalisar, domin yana daga cikin wadanda aka rika fadi tashi ta shi da shi wajen kai ziyarar tuntuba ga wasu daga cikin shugabanni a kasar.
Zargin Almundahana: Hukumar yaƙi da cin haci ta kama kwamishinan Ganduje da wasu mutane 5
Shi ma Sanata Rufi’i Sani Hanga duk da dai bai taka irin rawar da Madakin gini ya taka ba, amma shi ma rahotanni sun bayyana cewa Godswill Akpabio ya zaba a matsayin shugaban majalisar Dattawan Nigeria, Inda har aka rika ganin kamar yin hakan da yayi ya sabawa umarnin da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Rabi’u Musa Kwankwaso ya basu na zama tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Abdul’aziz Yari.
An zargi hakan ne saboda yadda Sanata Abdul’aziz yari, ya ziyarci Kwankwaso kuma har sun Kulle kofa sun yi tattaunawa ta musamman kan neman goyon bayan yan majalisar dattawa guda biyu daga Kano, Sanatan kano ta kudu Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila da Sanatan kano ta tsakiya Rufi’i Sani Hanga.
Yanzu dai mai faruwa ta riga ta faru abun zuba Ido a gani shi ne ta yaya wadannan mukamai na Hanga da Madakin gini zasu taimakawa al’ummar jihar kano.