Abba Gida-gida ya bayyana lokacin da za’a fara tura ɗalibai kasashen waje

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yace ɗaliban da gwamnatinsa zata ɗauki nauyin Karatun digirinsu na biyu zasu fara harkokin karatunsa a watan Satumba na wannan Shekarar.

 

Gwaman ya bayyana hakan ne lokacin da karɓi bakuncin Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda ya kai masa ziyarar barka da Sallah a gidan gwamnatin kano.

Wasan taya Murnar Karin Girma: Mazauna gidan Yari na kurmawa sun lallasa Ma’aikatan gidan gyaran hali

Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na baiwa Ilimi fifiko, Inda yace daga hawansa kan mulki ya sake buɗe makarantu 20 da gwamnatin data gabata ta rufe , tare da sake bude makarantun koyar da harkokin addinin musulunci na kananan hukumomin 44 dake jihar kano domin samar da ingantaccen ilimi ga al’umma.

Tallah

Gwamna Abba Kabir ya kuma godewa Sarkin saboda wannan ziyarar ,sannan ya yabada da irin rawar da sarakunan gargajiya suka tawa wajen Adana tarihi da al’ada da zaman lafiya da cigaba a jihar kano.

 

Da yake nasa jawabin Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ya ce ya Kai ziyarar ne domin yiwa gwamnan jihar kano Barka da Sallah, sannan ya bukaci gwamnatin jihar data samar da taki ga manoma don inganta harkokin noma kano.

Sarkin Bichin ya kuma bukaci gwamnatin da ta samar tsarin wayar da kan mutane akan muhimmancin dashen bishiyoyi da samar da rijiyoyin burtsatse a yankunan karkara don inganta rayuwar al’ummar.

Sarkin ya yabawa gwamnan jihar kano bisa nada Dr. Baffa Bichi a matsayin Sakataren gwamnatin jihar kano, sannan Kuma ya bukaci masu zuba jari da su zo kano domin zuba jari don inganta tattalin arziki jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...