Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Wasu masu gine-gine a jihar Kano na ci gaba da bayyana halin damuwa da firgici da suke ciki, sakamakon yiwuwar rushe musu gine-ginen su daga nan zuwa kowanne lokaci.
Masu irn wadannan gidaje sun ce tuni an shafawa gine-ginen nasu jan fenti na gargadi, wata alama ce da ke nuna cewa daga nan zuwa kowanne lokaci za a iya zuwa a rushe musu gidajen nasu.

Wani magidanci a unguwar Salanta dake kanon ya bukaci gwamnatin da ta duba wannan al’amari duba da halin da suka tsinci kansu.
Allah yasan halin da muke ciki, don haka ku mayar da komai gare shi – Tinubu ya fadawa Yan Nigeria
A cewarsa ”Ni ba dan siyasa ba ne, kuma ‘yan unguwar nan gwamnati suka zaba, an bi mu kasuwa yanzu an biyo mu gida za a hana mu barci, ya kamata a duba wannan lamari, mun bi ka’ida amma ana son a fitar da mu daga gidajenmu”.

Abun da gwamnati ke cewa
Ita dai gwamnatin jihar Kano karkashin Engr. Abba Kabir Yusuf, na zargin cewa an yi gine-ginen ne ba bisa ka’ida ba, a filayen al’umma, don haka take kokarin kwacewa don mayar da su ga jama’ar Kano.
BBC Hausa ta rawaito Sakataren gwamnatin jihar Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya bayyana cewa gwamnatin ba wai rusau take yi ba, gyara ne take yi.
”Lallai-lallai ya kamata al’umma su yarda cewa wuraren da aka ware a matsayin makarantu, ko asibitoci, ko makabartu ba wurare ne da wani zai zo ya yanka don yana da wani mukamin gwamanti ya sayar ba”. in ji shi.
Ya kara da cewa ”Babu yadda za a ce kana gani a tsaga makaranta a sayar maka, ga dakin karatu ga azuzuwan yara amma ka saya ka gina gida, wannan abu ne da ya saba ka’ida, don haka abin da muke kokarin yi shi ne mu karbe mu dawowa da mutanen Kano kayansu”.
”Akwai asibitin fa da gidajen likitoci aka rushe aka gina gidan biki, akwai makarantar da aka kori dalibai aka sayar da makarantar, aka mayar da su kauye, yanzu fisabilillah da ace gwamnonin da suka gabata haka suka yi shi ina zai samu inda zai sayar?” in ji Dr Baffa.
Tun dai kafin a rantsar da shi a matsayin gwamna ne, gwamnan na Kano Abba Kabir Yusuf ke gargadi ga masu gine-gine a filayen gwamnati a jihar su daina.
Kana ya yi yakin neman zabe da alkawarin idan ya samu nasara, zai kwace filayen da jam’iyyarsu ta NNPP ke zargin gwamnatin Ganduje da ta gabata ta sayar wa makusantanta ba bisa ka’ida ba.