Daga Kamal Umar Kurna
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kwashe sharar dake jibge akan tirin gidan sarkin Kano daura da gidan Dan masani dab da Kofar shiga Makarantar SAS a matsayin Wani muhimmin aiki wanda zai Kara fito da martabar Kano.

Shugaban kwamitin karta kwana na kwashe sharar jihar nan Alhaji Ahmadu Haruna zago, shi ne ya bayyana hakan a daren yau lokacin da jami’an hukumar kwashe shara ta jihar nan suka yi dirar mikiya a wajen domin gabatar da ayyukansu.
A cewar Dan zago hanyar zuwa gidan Dan masani da Kofar shiga Makarantar S.A.S, wurare ne masu matukar muhimmanci da tarihi ga al’ummar jihar nan, a don haka akwai bukatar Samar da kyakkyawan yanayi a wuraren domin samun cikakkiyar tsafta.
Ganduje ya Magantu kan dakatar da albashin ma’aikata dubu 10 da gwamnatin Kano ta yi
” Wannan kwamiti na mu yana aiki ba dare ba rana ne don mu tsaftace jihar kano da kuma magance cututtuka da shara take haifarwa, sanann kuma yin hakan zai kara fito da martabar jihar a idon bakin dake shigowa Kano kowacce Rana”. Inji shi
Dan zago daga nan sai ya bukaci al’ummar dake rayuwa a yankunan dasu kasance masu bin doka da oda ta hanyar kai sharar su wuraren da hukuma ta tanada domin zubarwa domin samarwa da kansu ingantacciyar rayuwa me cike da lafiya da tsafta.