Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya taya gwamna Abba Kabir Yusuf da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da sauran musulmin jihar murnar zagayowar bukukuwan Sallah babba.
Sakon Barka da Sallah na Gwarzo na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Ibrahim Garba Shuaibu ya fitar Kuma ya aikowa kadaura24 a ranar Laraba,

Ya ce a yayin da al’ummar musulmi a fadin duniya ke gudanar da murnar zagayowar babbar sallah , akwai bukatar Musulmi su yi amfani da lokacin wajen son juna tare da sanya farin ciki a zukatan masoyansu.
Tsohon dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP ya taya al’umma Kano murnar Babba Sallah
Kwamishinan wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar, ya bukaci al’ummar jihar da su marawa gwamnatin Gwamna Abba Kabir baya, yana mai cewa “Wannan gwamnatin ta daukacin al’ummar jihar ce. Dole ne mu ba shi goyon baya don cimma burin da ake so na maido da martabar jihar da ta bata”.
Ya kuma bukaci al’ummar musulmin jihar da su tabbatar da cewa suma sun tallafawa masu karamin karfi musamman a wannan lokaci na Sallah babba.

Gwarzo ya yi kira ga mabiya addinin Musulunci da su yi amfani da bikin wajen da yi wa Najeriya addu’a musamman ta fuskar tsaro da tattalin arziki.
Kwamishinan ya sake jaddada alkawarin gwamnati mai ci na samar da shugabanci nagari da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa domin zuba jari don bunkasa tattalin arzikin jihar da inganta rayuwar al’umma.