Allah yasan halin da muke ciki, don haka ku mayar da komai gare shi – Tinubu ya fadawa Yan Nigeria

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Shugaban ƙasar Najeriya Bola Tinubu ya amince da cewa Najeriya na fuskantar kalubale mai tarin yawa, amma kuma a cewarsa yana kokarin samar da hanyoyin magance matsalolin.

 

A cikin sanarwar da ya fitar na taya musulmin Najeriya murnar Barka da Sallah, Asiwaju Tinubu ya ce “Dole ne mu gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu damar halartar wata Sallar Idi”.

Tallah

Ya ƙara da cewa Allah ba ya ɗora wa mutum abin da ba zai iya ɗauka ba.”

“Allah Ya san halin da ƴan Najeriya ke ciki kuma zai kawo musu sauƙi.”

Jerin gwanon motocin Tinubu ya haifar da cece-kuce a Nigeria

Sannan ya buƙaci al’umma da su yarda cewa ƙasar za ta gyaru, su kuma haɗa hannu wajen cimma nasarar hakan.

Ya kara da cewa gwamnatinsa ta fara neman hanyar magance matsalolin da ke addabar kasar, ta hanyar shawarwarin da suke samu daga wajen kwararru don gyara tattalin arziƙi da kuma kawarda duk wani cikas da zai hana bunƙasar Najeriya.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...