Yadda Shirin da Hadiza Gabon ta ke gabatarwa ya tada Kura

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Fitacciyar jarumar Kannywood Hadiza Aliyu wadda aka fi sani da Hadiza Gabon, a yanzu haka tana gabatar da wani shiri da ke yawo a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke yin tsokaci da kuma yin tambayoyi kan abubuwan da suka kira ‘rashin kwarewa wajen gabatar da shirin .

 

Shahararriyar jarumar Kannywood din dai a hankali tana janyewa daga wasan kwaikwayo zuwa gabatar da wancan shiri wanda take tattaunawa da Shahararrun mutane, Inda ta Saka masa sunan “Gabon Room talk Show” ma’ana dakin gabatar da shirin Gabon.

Hajjin bana: Mahajjata 70,000 ne suka samu kulawar likitoci a Makkah da Madina -Saudiyya

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a farkon shekarar da ta gabata ne ta fara gabatar da shirin Inda ta sanya masa suna “Dandalin Hadiza Gabon”. An fara shirin ne a ranar 19 ga Satumba, 2022 kuma Hadiza Gabon ta fara tattaunawa da wata Sa’adatu Lawan.

Tinubu ya fasa dawowa Nigeria a yau Asabar

Ta kuma zanta da fitaccen mawakin Siyasar nan, Daudau Kahutu Rarara.

 

A hirarta da Rarara, ta tambaye shi dangantakarsa da abokinsa Abdul Amart Maikwashewa wanda ya ce yaronsa ne.

Daga baya Abdul Amart wanda shi ma ta gayyace shi cikin shirin ya musanta batun na Rarara, inda ya ce tun da farko a matsayinsa na furodusa yana amfani da kudinsa wajen shiryawa jarumai fina-finai da Kuma wakoki na bidiyo kuma cikin wadanda ya shiryawa har da shi Rarara din.

Jarumai masu shirya fina-finai da sauran yan Kannywood na ta tururuwar zuwa jerin shirye-shiryen Hadiza Gabon din a lokuta daban-daban .

Lamarin da ya jawo tsokaci daga masu amfani da yanar gizo a dan wannan lokaci shi ne, tattaunawar Gabon da mawaki El-mu’az Birniwa, inda ta tambaye shi game da abokiyar aikin sa Hannatu Bashir.

Tallah

“Kowa ya san Hannatu Bashir budurwarka ce haka ne ?.” tambayar ke nan da Gabon ta yiwa El-mu’az.

A fusace Birniwa ta ce, “A’a, sai dai in kina son ki sanar da su yanzu. Idan har kowa ya sani, to kenan babu buƙatar yi min tambaya akai. ”

Daga baya a cikin hirar Birniwa ya ce da ya san za ta yi masa irin wadannan tambayoyin, da bai amsa gayyatar da ta yi masa ba.

A karshen tattaunawar, Birniwa a wani abu mai kama da ramuwar gayya, ya ce kasancewar kina tallafawa mutane zamu so mu San a ina kike samun kudin da kike wannan aikin ?”

Ta amsa da cewa tana da sana’o’inta a gefe, wanda Allah ya sanya albarka.

Lokacin da ya dage kan sanin sana’o’in, ta ce tana harkar dinke-dinke, yin wasan kwaikwayo, sannan kuma tana gudanar da wani kamfani.

Bai gama tambayarsa ba, sai ya kara da cewa ita ba ta cikin masana’antar kamar da, kuma ya san shagonta a Kaduna, amma mutane zasu bukaci sanin sauran kasuwanci da take yi da kamfanin da ta ambata.

Da take mayar da martani, wata Malama a Jami’ar Jihar Bauchi, Dakta Furera Bagel, ta rubuta a shafinta na Facebook cewa, “Ina ganin Hadiza Gabon ta rude kan me ya kamata ta yi a matsayinta ta mai gabatar da shirinTalk Show. Watakila ta kasance tana kallon Hard Talk na Mahdi Hassan ko kuma na Channels kuma tana son ta maida kanta yar jarida.

Matsala ita ce, ba na jin wani daga cikin waɗancan mashahuran da suke halastar shirinta suna yarjejeniya kan irin tambayoyin da zatai musu. Haba, don Allah! Wannan ai cin zarafi ne kuma yana iya haifar da rudani a cikin gidan aure!” Da take tsokaci kan hira da Birniwa.

Wani marubuci, mai suna Na-Allah Mohammed Zagga, ya ce “Salon hirar Hadiza Gabon abun dubawa ne: ya rubuta yace “kowa yasan budurwar kace.” Kowa ya san za ku fita da ita. Kai! Ta yaya za ku yi wa mai aure irin wannan tambayar? Kowa? Idan Zagga da sauransu ba su sani ba kuma fa? Shin wannan hira ce ko titsiye? Ka yi tunanin ace Gabon tana da aure kuma wani mai gabatar da shiri a TV ya gaya mata cewa ‘kowa ya san cewa za ku fita da furodusan ku’. Me kake tunani mijinta zai dauka.

“Ina ma’anar fa’idar wanann shiri ? Idan zarginta ya lalata auren mutumin fa? Bai dace ba yin tambayoyi da yawa game da rayuwar mutum ta sirri maimakon mayar da hankali kan nasarorin da ya samu ko gazawarsa a harkar fim. Dole ne ku mutunta haƙƙin sirrin baƙonku. Bai kamata rika yiwa bakonku tambayoyin da basu da alaka da rayuwar sa ta zahiri ba ko dan Saboda masalahar al’umma .”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...