Yanzu-Yanzu: Tinubu ya rushe majalisun gudanarwar Hukumomi, ma’aikatu da kamfanonin gwamnatin tarayya

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da rushe dukkanin majalisun gudanarwa na hukumomi da ma’aikatu, cibiyoyi da kamfanonin gwamnatin tarayya, ba tare da bata lokaci ba.

 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey a daren ranar Litinin a Abuja.

Da dumi-dumi: Tinubu ya sauke Hafsoshin tsaron Nigeria , ya kuma nada sabbi

Sanarwar ta ce, hakan yayi dai-dai da karfin ikon da kundin tsarin mulkin kasar ya baiwa shugaban kasa don amfanin jama’a.

Yanzu-Yanzu: Abba Gida-gida ya sake sabbin nade-naden mukamai

‘’Rushewar ba ta shafi kwamitoci da kuma Majalisun da aka tsara a Jadawali na Uku, Sashi na 1, Sashi na 153 (i) na Kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ba,’’ in ji sanarwar.

Dangane da wannan an umarci shugabannin ma’aikatu, Hukumomi, Cibiyoyi, da Kamfanonin Gwamnatin tarayya da cewa yanzu duk abun da zasu yi wanda zai majalisar gudanarwar su ta sani to, manyan Sakatarorin ma’aikatun su turawa Shugaban kasa ta karkashin ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

Tallah

” Don haka, dukkan Ma’aikatu su tabbatar da bin wannan umurnin da zai fara aiki daga ranar Juma’a 16 ga watan Yuni, 2023″.

An umurci manyan sakatarorin da su sanar da shugabannin hukumomin da abin ya shafa a karkashin kulawar ma’aikatu/Ofisoshinsu domin a su bi umarnin cikin gaggawa .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...