Daga Kamal Yakubu Ali
Wani malamin addinin musulunci a kano sheikh Bashir Bakin Ruwa, ya bukaci iyaye da su kara maida hankali wajan tallafawa makarantun addinin musulunci duba da irin gudunmawar da suke bayarwa wajan samarda al’umma ta gari .
Sheik Bakin Ruwa ya bayyana hakan ne yayin bikin saukar karatun alkurani mai girma na daliban makarantar Raudatul kur’ani murattal bangaren Asuba da ummahatu karo na 2 na dalibai 17 wanda ya gudana a farfajiyar makarantar dake unguwar mai Aduwa dake karamar hukumar Dala.
Yanzu-Yanzu: Abba Gida-gida ya sake sabbin nade-naden mukamai
Sheikh Bakin Ruwa yace marigayi sheikh Abubakar Ramadan shi ne ya Assasa wannan makaranta domin yada ilimin addini musulunci da samar da mahaddatan alkurani da kuma kara chusa kaunar Annabi sallallah Alaihi wasallam da sahabbansa a zukatan al’ummar Musulmi .
Ya bukaci daliban dasu kara zage damtse wajan neman ilimi a fannoni daban-daban na rayuwa, domin samun kyakyawar rayuwa a duniya da lahira.

Wasu Daga cikin daliban da suka samu sasarar saukar karatun alkurani sun hadar da Muhammad musa Dattijo Mai kimanin shekaru 60 da sauran manyan mutane, inda suka bayyana cewa tsofa bai hana so zuwa makaranta ba, kuma sun samu
Taron ya samu halarta al’umma da dama wadanda suka hadar da Alhaj Bature yahaya da sharif Auwal mahir sharif bala da sauran manyan limaman dake fadin jahar nan.