Zabe Gwamnan Kano: Kotu ta amince da bukatar APC, na duba na’urar BVAS

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kano, a ranar Juma’a, ta amince da rokon da jam’iyyar APC ta Kano shigar, na bada damar duba na’urar BVAS, da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi amfani da ita a zaben 18 ga Maris, 2023 a jihar.

 

Alkalan guda 3, sun bayar da izinin duba na’urar BVAS da akai amfani da su a kananan hukumomin Bebeji, Gezawa, Tudun Wada, Garko, Ungogo, Ajingi da Bunkure, Warawa da Karaye.

 

Justice Watch News ta rawaito cewa jagoran Lauyan masu shigar da Kara Nuraini Jimoh SAN ya shigar da bukatar yana neman kotun ta baiwa APC damar duba na’urorin kananan hukumomin da abin ya shafa tare da na’urar BVAS, yayin zaben Gwamnan Kano da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya yi sabbin nade-naden mukamai

A hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Osadebay ta ce bayan ta duba dukkan hujjojin da lauyoyin biyu suka gabatar, ta tabbatar da cewa masu shigar da kara sun yi roko a sassa da dama na kokensu.

 

Ta ci gaba da cewa bayar da damar ba zai kawo targaro a sauraron Shari’ar ba.

Gwamnatin Kano za ta rushe Masarautun Gaya, Rano, Bichi da Karaye da Kuma dawo da Sarki Sunusi

” Rashin basu damar duba na’urorin na BVAS kamar yadda suka roka, ya sawaba sashi na 146 na Dokar Zabe, 2022 da aka yiwa gyara.”

Hakazalika kotun ta yi watsi da rokon dukkanin bangarorin su hadu ya yin duba na’urar ta BVAS.

Don haka, wadanda ake kara a cikin koken sun shigar da bukatar neman kotun ta yi watsi da karar saboda zargin da ake yi na rashin nasara.

A jawabansu daban-daban, Lauyan hukumar INEC, Barista KC Wisdom, Engr Abba Kabir Yusuf, BJ Akomolafe SAN da NNPP Barista Abdulhamid Mohammed, sun bayyana cewa daukar nauyin takara da tsayar da dan takara lamari ne kawai na jam’iyya, inda suka jaddada cewa ba lallai ba ne sai sunan mutum ya bayyana a rijistar INEC .

Lauyan ya ci gaba da cewa sashi na 171 da na 172 na CFRN yayi bayyani a kan cancantar takarar jam’iyya a zabe, inda ya yi zargin cewa babu wata jam’iyya da ya kamata ta ci gajiyar tallafin da kotun ta bayar.

Ya ci gaba da cewa jam’iyyar APC ba ta da dan takara inda ya bukaci kotu da ta yi watsi da karar da aka shigar na rashin samun gurbi domin kalubalantar nasarar Engr. Abba Kabir da jam’iyyar sa ta NNPP.

.

A nasa martanin, lauyan mai shigar da kara, Nuraini Jimoh ya bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar wadanda ake kara saboda rashi hujja mai gamsarwa.

“Ya mai Shari’a APC ce kadai jam’iyya a gabanku, sashe na 136 na dokar zabe ta 2022 ya bamu mafakar cewa duk dan takarar da ya zo na biyu ya zo.”

A yayin da yake mayar da martani kan hujjar cewa sunan Engr Abba Kabir Yusuf ba ya cikin jerin sunayen ‘yan jam’iyyar NNPP da aka aika wa INEC, Nuraini Jimoh ya ce doka ta 177 ta 2022 ta ce dole ne mutum ya cancanta ya tsaya takara a jam’iyyar siyasa. mamba mai rijista kwanaki 30 gabanin zaben fidda gwani, inda ya dage da cewa ba a saka sunan Abba Kabir a cikin rajistar membobin NNPP da aka aika wa INEC.

“Ya mai Shari’a idan ba a aika sunan dan takara zuwa INEC kwanaki 30 gabanin zaben fidda gwani ba wannan mutumin bai cancanci tsayawa takara ba.

Ina roƙon ku da ku yi watsi da bukatar wanda muke Kara na farko.” Nuraini .” Jimoh ya roki kotun

Alkalan kotun guda 3 karkashin jagorancin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay sun tanadi hukuncin har zuwa ranar da za’a yanke hukuncin Shari’ar baki daya, sannan kuma suka dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Yuni domin ci gaba da shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...