Daga Auwalu Alhassan Kademi
Gwamnatin jihar Kano ta ce rushe shatale-talen dake Kofar gidan gwamnatin jihar ne domin amfanin jama’a.
Kafin wannan aikin, gwamnati ta tuntubi kwararrun Injiniyoyi a fannonin da suka dace wadanda suka tabbatar da cewa ginin shatale-talen ba shi da inganci kuma akwai yiwuwar zai iya rugujewa ta 2024.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.
Hotuna: yadda Aka rushe shatale-talen dake Kofar gidan gwamnatin kano
Wannan ya faru ne saboda ana yin shi da kayan aiki marasa inganci, hakan tasa dole a rushe shi don sake gina wani wanda zai dace da Kofar gidan gwamnatin kano.
Har ila yau, shatale-talen ya yi tsayi da yawa, wanda hakan tasa yake kawo barazana ga sha’anin tsaron gidan domin yana hana na’urorin tsaro dake gidan yin aikin su yadda ya kamata.
Bugu da ƙari, yana haifar da cunkoson ababen hawa a yankin saboda girmansa, tare da hana direbobi gano abun da ke gabansu.
Gwamnatin ta bayyana cewa ya zama dole ta rushe shatale-talen domin sake gina wani cikin gaggawa da kuma rage masa tsaho don tabbatar da ganin kofar gidan gwamnati da kare lafiyar masu ababen hawa.