Ba yan Siyasa kadai ne ya kamata su rika tallafawa al’umma ba – Yusuf Hassan Darma

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Wani Dan kishin kasa da yake tallafawa al’umma musamman ta fuskar Ilimi Yusuf Hassan Darma, ya bukaci mawadata da suke cikin al’umma da su rika tallafawa matasa da sauran al’umma duba da matsin rayuwa da ake fuskanta.

 

“Ya kamata duk wanda Allah ya bashi dama to yana da kyau ya tallafawa al’umma duba da halin matsin rayuwa da al’ummar suke ciki a yanzu”.

 

Yusuf Hassan Darma ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilin Kadaura24 a ofishinsa dake Kano.

Hotuna: yadda Aka rushe shatale-talen dake Kofar gidan gwamnatin kano

Yace yana da kyau ace idan Allah yabaka dama ka tallafawa al’umma mussamman matasa domin a samar musu da gobe mai kyau, duba da halin matsin rayuwa da al’umma.

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

Yusuf Darma yace ba ‘yan siyasa kadai ke da alhakin tallafawa al’umma ba, kamata yayi duk wanda Allah ya hore masa yafi karfin abinda zaici to hakika ya chanchanta ya taimaki na kasa dashi domin da hakane kadai zai sa a sami sauƙi a cikin al’umma.

“Kasancewa ta matashi, ina baiwa matasa shawara dasu guji zaman banza domin su sami ingantacciyar rayuwa su daina yarda wani yayi amfani dasu wajen bangar siyasa ko shaye-shaye kasancewar shaye-shaye hanya ce yin duk wani laifi”. Inji Yusuf Darma

Daga karshe yayi kira ga gwamnati da tabijiro da wani tsari da matasa zasu amfana mussamman wajen kaisu makarantu ko wata hanya da zasu koyi sana’o’i domin su dogara da kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...