12 June: Yau Najeriya take Bikin Ranar Dimokuradiyya

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Ranar 12 ga watan Yuni, ita ce ranar da gwamnatin Najeriya ta kebe domin gudanar da bikin ranar Dimokuradiyya a kasar.

 

Wannan rana ce da tarihin kasar ba zai manta da ita ba saboda a ranar ne aka gudanar da zaben Najeriya na 1993, ko da yake har kawo yanzu hukumar zaben Najeriyar ba ta sanar da wanda ya ci shi ba.

 

To sai dai kuma alamu sun nuna cewa dan takarar jam’iyyar SDP, wato Moshood Kashimawo Olawale Abiola, ne ya lashe zaben inda ya kayar da abokin takararsa na jam’iyyar NRC Bashir Othman Tofa.

Hajjin bana: Dalilin da suke sanyawa ake dage rigar dakin ka’aba

An dai ki sanar da sakamakon zaben ne saboda soke zaben da gwamnatin mulkin soja a karkashin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi.

Soke zaben dai ya janyo gagarumar tirjiya daga ‘yan jam’iyyar SDP da kuma ‘yan gwagwarmaya da ke da rajin kafa gwamnatin farar hula a wancan lokaci abin da ya kai ga tsare wasunsu da dama ciki har da Abiola.

Wasu ‘yan kasar dai sun bayyana ranar a matsayin ranar da ta fara tabbatar da mulkin dimokaradiya a ƙasar.

Mannir Dan-Ali, tsohon ma’aikacin BBC ne, ya ce ranar ta June 12 ta haifar da dorewar dimokuradiya da siyasa da ma ci gaba a Najeriya, duk kuwa da cewar akwai matsaloli nan da can.

Mannir Dan-Ali, ya ce,” Babbar alamar ci gaba ma shi ne dorewar mulkin farar hula ko da kuwa ba duka ka’idojin dimokuradiyya ake bi ba.”
Wannan rana ta 12 ga watan Yuni, ta kara karfi ne bayan da gwamnatin mulkin dimokuradiyya ta zauna da kafarta a 1999.

An rinka gudanar da bikin wannan rana ne tun daga shekarar 2002, haka kuma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara wa wannan rana karfi a shekarar 2018 bayan da ya sauya ranar dimokuradiyya daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa ranar 12 ga watan Yuni.

Sauya ranar Dimokuradiyya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni bai yi wa wasu ‘yan Najeriyar dadi ba inda har wasu na ganin cewa siyasa ce kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...