Daga
Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya ta DSS ta ce yanzu haka ba ta tsare da tsohon Gwamnan Babban Banki (CBN) Godwin Emefiele.
Tun a daren jiya Juma’a wasu rahotanni suka ce jami’an tsaron sun yi awon gaba da shi jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi daga muƙaminsa.
“Yanzu haka, Emefiele ba ya tare da mu,” in ji hukumar cikin wani saƙon Twitter.
Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamnan CBN, Emefiele
Ba wannan ne karon farko da rahotanni ke alaƙanta tsohon gwamnan da DSS ba, musamman tun bayan da ya ƙaddamar da shirin sauya takardun naira da kuma rage yawan ganin kuɗin a hannun mutane bisa amincewar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Da dumi-dumi: Kwankwaso ya bayyana abubuwan da suka tattauna da Shugaba Tinubu
Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan bankin ne nan take cikin wata sanarwa, inda aka umarce shi da ya miƙa ragamar CBN ɗin ga mataimakin gwamna mai kula da harkokin gudanarwa, Folashodun Adebisi.
Mista Adebisi zai kasance muƙaddashin gwamna har sai an kammala binciken zarge-zarge a kan Emefiele da kuma sauye-sauye a bangaren kuɗi, kamar yadda sanarwar ta bayyana.