Daga Aliyu Danbala Gwarzo
shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) a ranar juma’ar nan.
Daraktan yada labaran ofishin Sakataren gwamnatin tarayya Willie Badsey ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Da dumi-dumi: Da na sami Kwankwaso a fadar shugaban kasa da na dalla masa Mari – Ganduje
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin kasa, Mista Godwin Emefiele, CFR, daga aiki ba tare da bata lokaci ba,”
“Wannan ya biyo bayan binciken da ake a ofishin da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a bangaren hada-hadar kudi na tattalin arzikin Nigeria.
An umurci Mista Emefiele da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Mataimakin Gwamnan mai kula da sashin Ayyuka), wanda zai yi aiki a matsayin Gwamnan Babban Bankin kasar har sai an kammala binciken.”