Daga Auwal Alhassan Kademi
A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawar sirri tsohon gwamnan da Rabiu Kwankwaso wanda ya yiwa jam’iyyar (NNPP) takarar shugaban kasa.
Kwankwaso, wanda tsohon Ministan Tsaro ne, Kuma suna da kyakyawar alaka da Tinubu, wanda a lokuta daban-daban ya bayyana shugaba mai ci a matsayin mai wanda yasan dabarun iya mulki, inji kamar yadda Daily Post ta rawaito.
Kadaura24 ta ruwaito ko a kwanakin baya kafin rantsar da shugaban ƙasar sai da Kwankwaso suka gana da shugaban ƙasar a birnin faransa.
Sai dai ganawar Tinubu da Kwankwason ta jawo cheche-chekuche a jihar kano, musamman yadda aka tsinkayi wata murya da ake zargi ta tsohon gwamnan kano Ganduje yana kokawa game da ganawar Tinubu da Kwankwason.
Kwankwaso ya nemi kotu ta kawace Nasarar wani dan majalisar tarayyar NNPP a Kano
Nan gaba zamu kawo muku labarin yadda ganawar ta kasance.