Da dumi-dumi: Da na sami Kwankwaso a fadar shugaban kasa da na dalla masa Mari – Ganduje

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon aya

 

Tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce da sami Engr. Rabiu Musa Kwankwaso, a fadar shugaban kasa da ya mare shi .

 

Kadaura24 ta ruwaito Kwankwaso ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar shugaban kasa a ranar Juma’a.

Yanzu-Yanzu: Tinubu na ganawa da Kwankwaso a fadar shugaban kasa

Yayin da yake zantawa da manema labaran fadar shugaban kasa, bayan ganawarsa da Tinubu kan matsalar tsaro a jihar Kano biyo bayan rushe gine-gine da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi, Ganduje ya nuna rashin jin dadinsa.

Kwankwaso ya nemi kotu ta kawace Nasarar wani dan majalisar tarayyar NNPP a Kano

“Na san yana cikin gidan amma ba mu hadu ba. Watakila da mun hadu da zan iya marin shi.”

Daily trust ta rawaito Ganduje ya ce an yi rushe-rushen ne ba tare da gudanar da wani bincike ba ko kuma bayar da sanarwar da ta dace daidai da tanadin dokar amfani da filaye ta jihar.

Tsohon gwamnan ya ce ya yi dogon bayani a kan lamarin yayin da ya ke bai wa shugaban kasa labarin, ya kuma kai karar sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, da shaidar bidiyon yadda aka yi wawason dukiyar jama’a da barnar da ita.

Ya ce Gwamnan wanda ya bayyana a matsayin “Solo” Kwankwaso bai ji dadi ba saboda Allah wadai da aka yi masa.

Kadaura24 ta ruwaito cewa gwamnan jihar Kano ya ce aikin rushe gine-ginen ya yi su ne domin cika alkawarin da ya dauka na inganta binin kano yayin yakin neman zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...