Janye tallafin mai: Gwamnonin jihohi na rage kwanakin aiki

Date:

Gwamnan jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya Godwin Obaseki ya rage kwanakin aikin gwamnti a faɗin jihar daga wuni biyar zuwa uku a mako.

 

A wata sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ranar Talata ta ce matakin wani ɓanagare ne na rage wa ma’aikata raɗaɗi da matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi zai haifar.

 

Sanarwar ta ci gaba da cewa “a matsayinmu na gwamnati mai hangen nesa, mun fara duba batun ƙarin albashin ma’aikatan jiharmu daga 30,000 zuwa 40,000 mafi ƙaranci, wanda ya zarta na kowacce jiha a ƙasarmu”.

“Haka kuma muna son tabbatar muku da cewa za mu ci gaba da biyan wannan kuɗi, yayin da muke fatan ƙara albashin, idan jiharmu ta fara samun kasonta daga kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta tara daga kuɗin cire tallafin man”, in ji sanarwar

Kungiyar ƙwadago ta bayyana dalilan da suka sa ta janye tafiya yajin

Haka kuma gwamnatin jihar ta ce tana sane da irin wahalhalun da matakin cire tallafin man ya haifar wa al’ummar jihar sakamakon ƙarin kuɗin mota da na abinci da ma’aikatan jihar ke fuskanta.

”A don haka ne gwamnatin jiha ke sanar da cewa ta rage wa ma’aikatan jihar kwanakin aikin gwamnati daga wuni biyar zuwa uku, inda za su yi aikin wuni biyun daga gida daga yanzu har zuwa wani lokaci nan gaba”, in ji sanarwar.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da wata jiha a ƙasar ke rage adadin kwanakin aikin gwamnati ba, domin rage wa ma’aikata raɗadin cire tallafin man fetur ba.

Ko a farkon makon da muke ciki ma gwamnatin jihar Kwara da ke arewacin ƙasar ta amince da ɗaukar matakin wucin-gadi na rage adadin kwanakin aikin gwamnati zuwa uku a mako, domin rage wa ma’aikata raɗaɗin da janye tallafin man fetur zai haifar.

Sanarwar ta gwamantin jihar fitar ta umarci shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ke faɗin jihar su gaggauta tsara wa ma’aikatansu kwanakin da ya kamata su je aiki.

Ko a farkon makon nan sai da gwamnatin jihar kwara ta rage kwanakin zuwa aiki daga kwanaki biyar zuwa uku domin saukakawa ma’aikatan jihar wahalar tsadar man fetur da faru sakamakon janye tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu ya Sanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...