Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya gana da manyan ‘yan kasuwar mai a fadar shugaban kasa dake Abuja a ranar talata.
‘Yan kasuwar sun samu jagorancin Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun, wanda shi ne Shugaban kungiyar masu sayar da mai.
Ganawar da shugaban kasar ya yi da ‘yan kasuwar mai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan cire tallafin man fetur.
Da dumi-dumi: Bola Tinubu ya Magantu kan rushe gine-gine da gwamnatin Abba Gida-gida ke yi a Kano
Shugaban kasar a yayin jawabinsa a ranar 29 ga watan Mayu a dandalin Eagle Square da ke Abuja ya sanar da cire tallafin man fetur. Shugaban ya ce gwamnatin da ta shude ta Muhammadu Buhari ba ta yi tanadin cire tallafin a kasafin kudin 2023 da ya wuce .