Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya nada kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a matsayin shugaban ma’aikatansa.
Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin tarayya Abiodun Oladunjoye ya fitar a wannan rana ta juma’a.
An nada Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata.
A ganawar da ya yi da kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC a yau a Abuja, shugaban ya kuma nada tsohon gwamnan jihar Benue kuma tsohon ministan ayyuka na musamman, George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya (SGF).
Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban ya nada tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu