Gwamna Zamfara ya musanta bayyana kadarorin Naira tiriliyan 9

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin jihar Zamfara ta musanta wani labari da aka yada a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa gwamnan jihar, Dauda Lawal ya bayyana kadarorinsa na Naira Tiriliyan Tara.

 

Majiyar Kadaura24 ta ruwaito cewa, gwamnatin cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ranar Juma’a a Gusau, ta bayyana labarin a matsayin mara tushe ballantana makama, Inda yace an shirya labarin ne domin kawar da hankalin sabuwar gwamnatin daga tafarkin Ceto Zamfara.

Sanarwar ya ce wadanda suka fadi zabe ne suka ƙirƙiri labarin, kamar yadda suka yi a lokacin yakin neman zabe.

 

Ya kara da cewa sabuwar gwamnati ta fara aiki kuma ta mayar da hankali wajen ganin ta inganta harkokin mulki a jihar domin gudanar da aikin da aka dora mata.

Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Kano ya kuma sanar da sabbin nada-naden mukamai

Sanarwar ta kara da cewa: “An ja hankalinmu kan wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo na cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana kadarorin da ya kai Naira Tiriliyan Tara, hakan tasa Gwamnati ta ta fitar da wannan sanarwa domin karyata wadanda masu bata lokacin su akan abun da bazai amfani al’ummar jihar Zamfara ba.

“Wannan karya ce da aka kirkira kuma aka tura ta a kafafen sada zumunta ba gaskiya ba ne ta hanyar bata gari da ke da niyyar karkatar da hankalin sabuwar gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...