Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Wani basarake mai rajin samar da sauƙi ga al’umma Amb. (Dr) Yunusa Yusuf Hamza Falakin Shinkafi ya ƙalubalanci masu gidajen da suke sayar da tsohon man fetur din da suka sayo da tsohon farashi akan sabon farashi.
” Wannan matakin da aka dauka babu Shakka zai sanya masu karamin karfi a cikin mawuyacin hali, saboda zai taba bangarori daban-daban na rayuwar al’umma musamman kayan masarufi da suka zama wajibi ga kowanne Dan Adam”. Inji shi
Falakin Shinkafin ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24 a Kano.
Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Kano ya kuma sanar da sabbin nada-naden mukamai
” A baya NNPC ta fadawa mutanen Nigeria cewa, tana da man da za’a iya amfani da shi har nan da watanni uku masu zuwa, don haka ban ga dalilin da zai sa a fara sayarwa yan Nigeria da tsohon man a sabon farashin ba”. Inji Amb. Yunusa Yusuf Hamza
Falakin Shinkafin wanda kuma shi ne Sardaunan matasan arewacin Nigeria ya bukaci gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu Tinubu da ta ɗauki matakan da suka dace, don saukaka al’ummar Nigeria.
Yace su kuma masu gidajen mai suma ya kama su ji tsoron Allah, su kuma sani cewa sai Allah ya tambayesu kan mawuyacin halin da suka jefa yan Nigeria a ciki, saboda tsohon man da gwamnati ta biya masa tallafi suke sayarwa al’umma a kan sabon farashi na Naira 540 ko ma sama da haka.