Babban Bankin Najeriya (CBN) ya musanta wani rahoto da ake yadawa cewa ya karya darajar Nigeria zuwa naira 630 a kan dala ɗaya.
Wata sanarwa da muƙaddashin darektan sadarwa na bankin, Isa AbdulMumin, ya fitar ya ce ko a jiya Laraba ma an sayar da kuɗin ne a kan naira 465 kan kowace dala saɓanin abin da wancan rahoton ya ce naira 630.
Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Kano ya kuma sanar da sabbin nada-naden mukamai
Sanarwar ta ce rahoton da wata jarida ta yi wanda ta ce ta samu bayaninsa ne ita kadai yana cike ne da karerayi da kuma jahilcin rashin sanin yadda kasuwar hadadar kudaden waje ta Najeriya take.
Darektan ya jaddada matsayar bankin a kan lamarin inda ya ce ko a safiyar yau an sayar da naira 465 a kan dala ɗaya.
Bankin ya shawarci jama’a da su yi watsi da rahoton wannan jarida da cewa ta yi ne da nufin haddasa firgici a kasuwar musayar kuɗaden.