Sabon Sakataren zartarwar Hukumar alhazai ta Kano ya kama aiki

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Sabon Sakataren zartarwar na hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano Alhaji Lamin Rabi’u ya kama aiki a yau din nan bayan nada shi da sabon gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi .

 

Yayin da yake jawabi Sakataren zartarwar ya godewa Allah subhanahu wata’allah bisa yadda ya baiwa gwamnan Kano ikon Mayar da shi hukumar domin sake hidimtawa alhazai bakin Allah.

” Ina kira ga ma’aikatan wannan hukuma da ku bani cikakken hadin kai kamar yadda kuka bani a baya, saboda mu FUTA Kunyar gwamnan da al’ummar jihar kano baki daya”. Inji Lamin Rabi’u

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Gida-gida ya yi Sabbin nada-naden mukamai

Lamin Rabi’u ya kuma bada tabbacin zai yi duk mai yiyuwa wajen wajen ganin an sami nasarar gudanar da ibadar aikin hajjin bana, Inda ya bukaci alhazan wanann shekara da su bada hadin kai don kyautata musu tun daga nan Kano har zuwa can kasa mai tsarki.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa a safiyar wannan rana gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya bada sanarwar nada Lamin Rabi’u a matsayin sabon Sakataren zartarwar na hukumar jin dadin alhazan jihar kano.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan ne karo na uku da Alhaji Lamin Rabi’u ya sake komawa hukumar a matsayin Sakataren zartarwa na hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...