Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Shugaban kasa Bola Tinubu zai fara aikinsa a matsayin shugaban Najeriya tare da ganawa da gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, da shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari a fadar gwamnatin tarayya .
Duk da cewa ba a bayyana makasudin taron a hukumance ba, jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa taron ba zai rasa nasaba da rikicin da ake samu na cire tallafin man fetur wanda tun daga lokacin ya jefa ‘yan Najeriya cikin fargaba.
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Gida-gida ya yi Sabbin nada-naden mukamai
Tinubu ya shiga fadar shugaban kasa a ranar Talata, inda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da wasu manyan jami’an gwamnati suka tarbe shi a kofar ofishinsa.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da kakakin majalisar Femi Gbajabiamila da babban sakataren fadar shugaban kasa Tijjani Umar, tsohon kwamishinan kudi na Legas, Wale Edun; Dele Alake; James Faleke.