Majalisar tsaro ta kano ta ayyana kwacen waya a matsayin fashi da makami

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Majalisar tsaro ta jihar Kano ta ayyana kwacen waya a matsayin fashi da makami kuma duk wani mutumin da aka kama za’a hukunta shi ne a matsayin dan fashi da makami .

 

Kadaura24 ta ruwaito cewa kwamishinan yada labarai mai barin gado, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano.

Da dumi-dumi: Akwai yiwuwar ni zan mika mulki ga sabon gwamnan kano – Ganduje

Ya ce majalisar, wacce Gwamna mai barin gado Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta a yayin zamanta ta nuna rashin jin dadin ta, bisa yadda kwacen waya ke Kara kazanta a yan kwanaki don haka akwai bukatar daukar tsauraran matakai don magance matsalar.

Malam Garba ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da samar da wata runduna ta musamman wacce zata rika aiki ba dare ba rana domin magance wannan matsala da ta addabi al’ummar a jihar.

Kwamishinan ya kara da cewa majalisar a yayin da take tattaunawa kan batun rantsar da sabon gwamnan ta ce an dauki dukkan matakan da suka dace don ganin an gudanar da bukukuwan lami lafiya, ya kuma yi gargadi masu shirin tada hatsaniya da su guji aikata irin haka domin jami’an ba za su saurarawa duk wanda aka kama ba.

Sanarwar ta kara da cewa, “ba za a amince da lalata kadarorin gwamnati da na daidaikun mutane ko ‘yan adawa ba saboda an dauki isassun matakan da za a bi wajen tunkarar wannan lamari cikin tsanaki.”

Ya ce a yayin taron, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jaddada bukatar mika mulki cikin kwanciyar hankali a jihar, tare da yin kira da a gudanar da bikin lami lafiya. Ya godewa jami’an tsaro a jihar bisa dukkan hadin kan da suka ba shi a tsawon lokacin mulkin sa, ya kuma bukace su da su kara zage damtse don kara inganta tsaro a jihar kano.

Taron ya samu halartar kusan dukkan shugabannin hukumomin tsaro da sauran mambobin majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...