Daga Isa Ahmad Getso
Gwamnan jihar kano mai barin gado Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce Akwai yiwuwar shi da kansa ne zai mika jihar ga sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Engr. Abba Kabir Yusuf a yau Lahadi.
” Muna nan Muna tuntubar juna kan yadda zan mika Kano ga sabuwar gwamnati, idan mun cimma matsaya ni da kai zan mika mulkin, idan kuma yanayi bai bada dama ba to Sakataren gwamnatin jihar kano shi zai mika musu mulkin kamar yadda doka ta tanada”. Ganduje
Kadaura24 ta rawaito Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabin bankwana ga al’ummar jihar kano a daren jiya asabar.
Ganduje ya bude gidan wutar lantarki mallakin kano
Ganduje ya kara da cewa kasancewa dukkanin bangarorin biyu na gwamnati mai barin gado da Kuma gwamnati mai jiran gado suna cikin uzurori daban-daban don haka ya ce idan hali yayi zai mika mulkin a Cikin daren wannan rana ta Lahadi.
Ganduje ya godewa al’ummar jihar kano bisa yadda suka bashi hadin kan da suka bashi har ya gudanar da aiyukan raya kasa da cigaban al’umma a tsahon shekaru 8 da yayi yana mulkin jihar.
” Da jam’iyyar mu ta APC ce zata gajemu da zan halarci bikin rantsuwar kama aiki na sabuwar gwamnati, Amma tunda Babu kyakyawan yanayi ba za’a ganmu a wajen bikin ranar rantsuwa ba, duk da dama kundin tsarin mulki bai ce dole sai gwamna mai barin gado yana wajen ba”. Inji Ganduje