Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan jihar Kano mai barin gado Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci bude gadar sama data tashi daga Kofar zuwa Kantin Kwari, wadda aka sanya mata sunan sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu.
” Mun gina wannan gada domin saukaka al’ummar wannan yanki da suke Fagge Kofar mata da kasuwar kwari, wadda ta taimaka matuka wajen rage tsunkoson musamman ga masu zuwa kasuwar kantin kwari da kuma sabbin shagunan da aka yi a filin idi”. Inji Ganduje
Da dumi-dumi: Akwai yiwuwar ni zan mika mulki ga sabon gwamnan kano – Ganduje
Da yake jawabi yayin bude gadar gwamna Ganduje ya ce an kashe sama da Naira Biliyan 7 domin gudanar da aikin gadar saboda da muhimmanci da take da shi , wajen saukaka zirga-zirga da inganta tattalin arzikin jihar kano.
” Mun bada dama an gina shagunan a filin idi saboda kullum burinmu shi ne cigaban jihar kano, amma akwai wadanda suka ce idan an rantsar da su zasu rushe shagunan hakan ya nuna basa kishin jihar kano don haka kar ku yarda su rushe”.
Ganduje ya ce titin gadar mai tsahon kilomita daya zai magance matsalolin cunkoson ababen hawan wanda yana kawo cigaba ga harkokin kasuwanci a kasuwannin dake yankin.
A dai wanann rana ta ƙarshe a mulkin Ganduje ya bude aiyukan da suka hadar da wani asibiti a garin warawa da Kuma Wani a unguwar hotoron kudu, da shagunan da aka gina a cibiyar yan jaridu ta kano, sai kuma sabon offishin hukumar zakka dake kan titin airport Road da titin coci Road sai kuma wasu aiyuka da garin Ganduje dake karamar hukumar Dawakin Tofa.