Daga Kabiru Yusuf
Awanni kadan kafin ya sauka gwamnan jihar Kano mai barin gado Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sabon kwamishina a hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar kano KANSEC.
Kwamishinan shari’a na jihar Kano Barr. M A Lawan ne ya rantsar da sabon kwamishinan mai suna Abdullah Abba Sumaila, yayin taron majalisar zartarwar jiha na ƙarshe wanda ya gudana daren jiya a gidan gwamnatin kano.
Da yake jawabi bayan rantsar da sabon kwamishinan gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce an rantsar da kwamishinan ne bayan majalisar dokokin jihar kano ta tantance tare da Amincewa da nada shi a matsayin kwamishina.
” Muna fata zaka yi aikin ka yadda ya dace saboda muhimmancin da hukumar zabe take da shi musamman wajen shirya zaben kananan hukumomi a jihar kano”.
An dai rantsar da sabon kwamishinan ne awanni kasa da 48 a rantsar da sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf.
Sai dai mukamin kwamishina irin wannan na wannan hukumar ba kamar sauran kwamishinoni na siyasa da aka Sani ba , domin shi wa’adi ne da shi na kamar yadda doka ta gindaya .